Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jami’an mu ba su kai hari kan fararen hula ba – Sojoji

Published

on

Rundunar sojin sama na ƙasar nan ta musanta wani rahoto da wasu kafafen ƴaɗa labarai suka yaɗa cewa, ta kai hari kan wasu jama’a da su ke tsaka da shagulgulan bikin aure a jihar Niger.

A cewar rundunar wannan labari ba gaskiya bane kuma an yi hakan ne don ɓata mata suna.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labarai na rundunar, Air Commodore Edward Gabkwet.

Sanarwar ta ce, wannan rahoto ba zai sanya rundunar ta saurara ba, a ci gaba da ayyukan da ta ke yi, na kakkaɓe ayyukan ta’addanci a Najeriya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!