Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

Matsalar NIN:- Dalibai su kammala yin rijistar daga 15 ga watan Yuni – JAMB

Published

on

Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantun kasar nan JAMB ta bukaci daliban da ke shirin rubuta jarrabawar da su kammala yin rajistar daga ranar 15 ga watan Yunin da muke ciki.

Wannan dai ya biyo bayan sanarwar sake karin wa’adin mako biyu na yin rajista ga daliban da suka fara rajista ta bana kuma suka samu matsala.

Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar a safiyar Litinin din nan, da ke bayyana cewa daga karfe 12 na ranar Litinin din, za a turowa da daliban cikakkun bayanai game da cibiyoyin da za su rubuta jarrabawar.

Kazalika sauran daliban da suka samu matsala za a sanar da su cibiyoyi na musamman da za su je su kammala rajistar su ko kuma ta kan layukan wayoyin su.

Sanarwar, wadda mai magana da yawun hukumar Fabian Benjamin ya sanyawa hannu, ta kuma ce, kowanne dalibi ya duba sako a shafin Internet na JAMB don samun karin bayani, musamman wadanda suka yi nasarar samun lambobin bayanan su ba tare da wata matsala ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!