Labarai
Jami’an tsaro na daukar matakai kan sake bullar yan Achaba- Kwamishina Waiya

Gwamnatin Jihar Kano ta ce hukumomin tsaro sun soma daukar matakai kan sake bullar ayyukan Achaba a sassa da dama na birnin Kano da kuma wasu yankuna da ke kan iyakar jihar, duk da an haramta sanaʼar tsawon lokaci.
Wannan na cikin sanarwar da Kwamishinan yaɗa labarai Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar a daren ranar Lahadi.
Sanarwar ta bayyana cewa sahihan bayanai sun nuna cewa, yawaitar masu amfani da babura wajen ɗaukar fasinja a unguwanni daban-daban, tare da samun rahoton wasu da ba a san su ba da ke shiga yankuna suna aiki a matsayin ƴan Achaba.
Ta ce gwamnati ta umurci hukumomin tsaro su karfafa matakan da suke dauka a dukkan kananan hukumomi 44 na jihar.
Sanarwar ta ce gwamnati ta ci gaba da bai wa hukumomin tsaro dukkan goyon bayan da ake bukata, tare da nazarin shawarwarin da jama’a suka bayar kan kara sa ido, musamman a hanyoyin shiga da fita daga Kano domin dakile lamarin.
You must be logged in to post a comment Login