Labarai
Jami’an tsaro ne suka tilasta min na amsa laifin kashe Hanifa – Abdulmalik Tanko
Malamin makarantar nan Abdulmalik Tanko da ake zargi da kashe dalibarsa Hanifa Abubakar ya ce, jami’an tsaro ne suka tursasashi ya amsa laifin da ake zarginsa.
Abdulmalik Tanko ya bayyana hakan a ranar Alhamis a gaban babbar kotun jiha Mai Lanba 5 dake sakatariyar Audu Bako Karkashin jagorancin mai Sharia mai Sharia Usman Na Abba.
A zaman kotun masu gabatar da kara sun ci gaba da gabatar da shaidu inda aka gabatar da jami’an tsaro daga sashin yaki da garkuwa da mutane kuma suka bada shaida.
Inda suka bayyana cewar sunyi musu tambayoyi batare da tursasamusu ba haka Kuma shima Abdulmalik Tanko ya bada bayaninsa inda ya bayyanawa kotu cewar shifa tilasata Masa akayi ya bada bayanansa a wancan lokaci.
Bayan kammala jin nasa bayanin itama Fatima Musa tace ganin abinda ya faru ga su Abdulmalik shi ne ya tsorata ta bada nata bayanin.
Daga karshe kotu taji bayanin kowane bangare bayanda Mai gabatar da Kara kwamishinan Sharia Barisata Musa Abdullahi Lawal yayi masa tambayar cewar duk bayanin daya fada a wajan bincike hakane? sai Yace haka ne.
Kotun ta dage ci gaba da zaman zuwa ranar 9 da 10 ga watan Maris na 2022 domin yin nazarin kotun.
You must be logged in to post a comment Login