Labarai
Jami’anmu na musamman za su sauka a Saudiyya yau- NAHCON

Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya NAHCON, ta ce, a yau Litinin ne tawagarta ta musamman za ta isa kasar Saudiyya domin fara gudanar da shirye-shiryen aikin Hajjin bana.
A cewar ta tsaikon tafiyar ta su da aka samu ya biyo bayan wasu gyare-gyare da ta yi da zai kara samar da ci gaba a aikin hajjin na bana.
Hakan na cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafukanta na Internet kan jinkirin tafiyar da aka samu.
Idan za a iya tunawa dai, a baya shugaban hukumar ta NAHCON Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya bayyana cewa a ranar 30 ga watan Afrilun da ya gabata ne Likitoci da masu kula da alhazai na musamman za su tafi kasar ta Saudiyya.
You must be logged in to post a comment Login