Manyan Labarai
Jami’ar Bayero ta kama dalibai shida da zargin magudin jarrabawa.
Hukumar gudanarwa ta Jami’ar Bayero, sashen tsangayar kimiyya da fasaha, ta gayyaci daliban tsangayar su shida bisa zargin su da aikata magudin jarrabawa.
Malamin da ke kula da shiryawa da rubuta jarrabawa na sashen nazarin kimiyyar na’ura mai Kwakwalwa, Sa’ud Adam Abdulkadir, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sa.
Malam Sa’ud Adam Abdulkadir, ya ce ana zargin daliban da aikata magudin jarrabawa da kuma samun takardar tambayoyin jarrabawa kafin ranar da za’a gudanar da jarrabawar.
Ya ce daliban za su bayyana a gaban kwamitin kula da rubuta jarrabawa na tsangayar ranar Litinin 11 ga watan Nuwambar da muke ciki domin kare kansu a kan zargin da a keyi musu.
Wakilin mu Anas Muhammad Mande, ya ruwaito ce wa an kama daliban yayin da a ke gudanar da jarabawar karshen zangon shekarar 2018/2019.