ilimi
Jami’ar Bayero ta ya ye Likitoci 133

Jami’ar Bayero dake nan Kano ta ya ye likitocin da suka karanci fannin kiwon Lafiya wato MBBS guda 118.
Haka zalika Jami’ar ta ya ye wadan da suka karanci fannin hakora wato Medical and Dental Science MDS guda 15, wanda ya kama jumulla guda 133.
Da ta ke basu rantsuwar zaman su cikakkun Likitocin shugabar hukumar dake lura da likitoci ta kasa Dakta Fatima Kyari ta bukace su da su kasance jajirtattu a kan aikin su ta yadda za su bawa kasar nan gudunmawa.
Fatima Kyari ta kuma ce dole sai sun kasance masu hakuri a aikin nasu idan har suna so suyi abin da ya dace.
Da ya ke jawabi shugaban Jami’ar ta Bayero Farfesa Sagir Adamu Abbas da mataimakinsa a fannin sanya idanu wato DVC Management Services Farfesa Aliyu Mu’azu yai magana a madadinsa cewa ya yi jami’ar na yaye jajirtattun likitocin da ake alfahari da su a Duniya, a domin haka ya bukaci sabbin likitocin da su ci gaba da rike kambun da Jami’ar ta ke da shi.
Shi kuwa a nasa jawabin shugaban kungiyar likitoci na kasa reshen Asibitin Aminu Kano NMA Dakta Abdurrahman Ali cewa ya yi kungiyar su za ta basu dukkan gudunmawar da ta kamata da za su ji dadin gudanar da aikin su.
A yayin taron bikin kaddamar da Likitocin da jami’ar ta Bayero ta yi an karrama wasu daga cikin su da suka nuna hazaka a lokacin da suke karatu.
Karo na 25 kenan da Jami’ar ta Bayero na ya ye likitoci a fannoni daban daban, inda kuma ta yaye na fannin hakora karo na 11 a yau Talata 04/03/2025
You must be logged in to post a comment Login