ilimi
Jami’ar Wudil za ta fara koyarwa daga gida – Farfesa Shehu Musa
Jami’ar kimiyya da fasaha da ke garin Wudul ta ce za ta fara koyar da ɗalibai karatu daga gida.
Shugaban Jami’ar Farfesa Shehu Alhaji Musa ne ya bayyana hakan ranar Asabar 12 ga Nuwambar 2021, yayin da yake rantar da sababbin ɗaliban makarantar da aka ɗauka karatun Digiri na gajeren zango da ake kira Part-time.
Farfesa Shehu Alhaji Musa ya ce makarantar ta dauki ɗalibai 830 da za su yi karatun na Part-time a ɓangarori daban-daban na jami’ar.
Ya kuma ja kunnen ɗaliban da aka ɗauka kan su kasance jakadu na gari a duk inda suka tsinci kansu.
Karon farko kenan da jami’ar ta Wudul ta fara bayar da karatun Digiri na Part-time ga ɗalibai.
You must be logged in to post a comment Login