Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jami’ar YUMSUK ta shiga sahun masu sharar tsaftar muhallin karshen wata

Published

on

Shugaba Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano ya ce duk wata jami’ar zata rinka yin gaggamin tsaftar muhalli a fadin makarantar baki daya.

Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa ne ya bayyana hakan yayin gaggamin tsaftar muhallin da ya gudana a Jami’ar.

Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa ya ce Jami’ar ta Saba gudanar da zagayen tsaftace muhallin daga lokaci zuwa lokaci, sai dai kuma a wannan karon ganganin ya janza salon, inda aka shigo da dalibai cikin tsarin.

Wanda ya ce ‘a baya daliban makarantar basu shiga cikin tsarin ba, wannan karon ne daliban suka shiga ayi dasu, wanda hakan ba karamin cigaba bane’.

Shima magatakardar wannan Jami’ar Isyaku Adamu cewa yayi ‘wannan gangamin zai taimaka wajen Samar da cikakkiyar tsaftar a makarantar, duk da cewa akwai wadanda aikin su ne tsaftace makarantar, sai dai girman da makarantar take dashi, indan suka hada hannu da su daliban, za’afi samun biyan bukata’.

A nasa bangaren shugaban walwalar dalibai na jami’ar Ibrahim Musa ya ce ‘daliban sun shiga ganganin ne duba da cewa idan an tsaftace muhallin makarantar, hakan daliban zai amfana kai tsaye.

A hannu guda shima shugaban dalibai na wannan Jami’ar Kwamret Tafida Sabo Akilu cewa yayi ‘tun zamanin da yake kamfen ya alkarwarta cewa daliban zasu shiga cikin sahun masu yin sharar duk karshen wata, wanda a wannan karon wakilan daliban ne suke fara halartar gaggamin, tare da SA ran wanda za’ayi nan gaba, dalibai sosai zasu shiga ayi dasu.

Freedom Radio ta rawaito cewa, yayin gangamin tsaftar muhallin shugaban makarantar, da masu rike da mukamai daban-daban, da kuma kungiyoyin dalibai da dama ne suka samu damar halartar gangamin tsaftar muhallin makarantar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!