Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zamu yi duk mai yiwuwa wajen magance matsalolin tsaro – Nigerian Navy

Published

on

Babban hafsan sojin ruwan ƙasar nan Vice Amiral Auwal Zubairu Gambo ya sha alwashin yin duk mai yiwuwa wajen magance matsalolin tsaron da ake fuskata.

Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin ruwan Commodore Sulaiman Dahun ya aike wa Freedom Radio.

Ya ce, babban Hafsan ya bayyana hakan ne lokacin da yake kare kasafin kuɗin rundunar na shekarar 2022 a gaban kwamimitin majalisar tarayya kan rundunar sojin ruwa.

Ya ƙara da cewar, rundunar ta yi ƙoƙari wajen magance barazanar satar mutane da fasa bututun mai.

Kazalika rundunar ta bada himma wajen yaƙi da masu ƙoƙarin kawo rashin tsaro a ƙasa.

Babban hafsan sojin ruwan ya bayyana yadda hukumar zata aiwatar da kasafin kuɗin na ta.

A ƙarshe Vice Admira Auwal Zubairu Gambo ya bayyana wasu ƙalubalen da rundunar ke fuskanta wajen gudanar da ayyukanta na rashin kayayyakin aiki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!