Connect with us

Labarai

Jami’ar Yusuf Maitama Sule zata fara Post UTME

Published

on

Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta sanar da cewa za ta fara aikin rajistar sabbin daliban da za ta tantance domin ba su gurbin karatu wato Post UTME a ranar laraba mai zuwa 26 ga wannan wata na Agusta da muke ciki.

Za a kammala aikin tantancewar a ranar 7 ga watan Oktoba mai zuwa, wato bayan shafe tsawo makonni 6 ana aikin, domin fara shekarar karatu ta 2020 zuwa 2021.

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai rikon mukamin magatakar jami’ar Malam Sulaiman Saleh, ta ce tuni aka fitar da adadin makin din da aka kayyade wa ko wane kwas da jami’ar take gudanarwa, kuma ta wallafa shi a shafinta na intanet www.nwu.edu.ng.

Sanarwar ta kara da cewa iya wadanda suke zabi jami’ar a matsayin gurbin farko wato first choice kadai za a baiwa damar yin rajistar domin shiga tantancewar.

 

 

 

 

 

AMA

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 335,289 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!