Labarai
Jam’iyar NNPP a Kano ta daukaka kara
Lauyan jam’iyyar NNPP mai Mulki a nan Kano Barista Bashir Yusuf Muhammad Tudun Wuzurci, ya ce sun kara daukaka Kara.
Tunda farko dai jam’iyyar adawa ta APC data shigar da kara ta bukaci kotun da ta basu damar gabatar da wani sheda a gabanta, abunda shikuma lauyan jam’iyyar NNPP,yayi suka akai,inda yace babu sunan sa a jerin shaidun dake gaban kotun, saidai kotun ta amince a gabatar da shedar.
A bunda ya sanya jam’iyyar NNPP,daukar matakin zuwa kotun daukaka domin ta tabbatar wa da kotun dake shari’ar haramacin gabatar da wannan shedar,kamar yadda lauyan jam’iyyar ta NNPPn yayi waakilin mu Aminu Abdu Bakanoma Karin bayani.
Rahoton: Yusuf Sulaiman
You must be logged in to post a comment Login