Labarai
Jam’iyyar ADC ta fitar da wa’adin karshe ga Atiku Babachir Lawal

Jam’iyyar hadaka ta ADC reshen Adamawa, ta fitar da wa’adin karshe ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, da sauran fitattun ‘ya’yan jam’iyyar.
Shugaban ADC na jihar, Shehu Yohanna, ne ya bayyana hakan in da ya ce dole su tafi mazabunsu su yi rajista kafin karshen shekara domin a gane su a matsayin sahihan ‘yan jam’iyyar.
Ya ce, babu wanda zai rike mukamin shugabanci a matakin kasa ba tare da ya mallaki katin jam’iyya ba. Yohanna ya kuma yi ikirarin cewa ADC ce kadai za ta iya karɓe mulki daga APC a shekarar 2027.
Rahotonni sun ce, an dakatar da rajistar Atiku a Jada tun bara, ba tare da wani gamsasshen bayani ba.
You must be logged in to post a comment Login