Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Jam’iyyar APC ta karyata rade-radin cewa tana shirye-shirye tsige mai alfarma sarkin musulmi

Published

on

Jam’iyyar APC ta jihar Sokoto ta karya ta rade-radin da ake yadawa cewa tana shirye-shirye tsige mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III daga kan mukamin sa, bayan an kammala zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jihar a ranar Asabar mai zuwa.

Jam’iyyar APC ta kuma yi watsi da matakin da wasu matasa suka dauka wajen yin zanga-zanga kan zargin da ake yi na shirin tsige mai alfarma sarkin Musulmin daga kan mukamin sa, da cewa wasu bata gari ne suka dauki nauyin su don kawai bata wa jam’iyyar suna.

Tun da fari a jiya Litinin ne wasu matasa suka gudanar da zanga-zanaga a cikin garin na Sokoto har zuwa fadar mai alfarma Alhaji Sa’d Abubakar III.

Da yake bayani yayin da suka isa fadar sarkin muslmin, jagoran matasan Murtala Abdulrahaman ya ce sun zo fadar sa ne don sheda masa cewa ana zargin kitsa tsige shi daga kan mikamin sa, kamar yadda ake ta rade-rade jam’iyyar APC a jihar ta Sokoto na shirin yi.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!