Connect with us

Labarai

Jam’iyyar APC ta naɗa Jamila Mai Wuƙa muƙamin SA

Published

on

Ofishin shugabar Matan Jam’iyyar APC ta ƙasa Mrs Mary ta nada Jamila Ado Mai Wuƙa a matsayin mashawarciya kan harkokin yaɗa labarai a yankin Arewa.

Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da Sakataren Ofishin shugabar Matan APC ta ƙasa Olugbenga Pius, ya fitar.

Sanarwar ta ruwaito cewa, naɗin ya zo a matsayin shaida ƙarara na ƙwazon aiki da jajircewar Jamila.

A cewar sanarwar, ƙwazon nata zai yi amfani matuƙa ga ofishin shugabar mata a jam’iyyar APC ta ƙasa.

Ofishin ya taya Jamila Ado maiwuka murnar samun wannan sabon ofishi a matsayin mashawarciya kan harkokin yada labarai SA a ofishin shugabar mata ta jam’iyyar APC ta kasa Mrs Mary Alile.

Sanarwar ta bukaci SA ta ci gaba da jajircewa wajen ganin an samar da ci gaba a jam’iyyar APC.

A cikin sanarwar ta yi Addu’a kan Allah ya ba su ƙarfi da basira don gudanar da ayyukan su a wannan ofishi.

Har zuwa naɗin nata, Jamila Ado Mai Wuƙa ta kasance ma’aikaciya a tashar Freedom Radio Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!