Connect with us

Labarai

Jam’iyyar hamayya ta PDP a Najeriya za ta gudanar da babban taronta duk da umarnin kotu da ta dakatar da su

Published

on

Babbar Jam’iyyar hamayya a Najeriya PDP ta ce za ta ci gaba da shirye-shiryen gudanar da babban taronta na zabe da aka tsara a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba, duk da sabon umarnin kotun tarayya da ta hana yin taron. Mataimakin sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Ibrahim Abdullahi, ya ce wannan hukuncin da kotu tayi bata lokaci ne kawai, yana mai cewa hukuncin kotun koli ya tabbatar da cewa jam’iyyun siyasa na da ikon gudanar da harkokinsu na cikin gida.

 

A ranar Talata, mai shari’a Peter Lifu na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya bayar da umarnin hana jam’iyyar PDP gudanar da taron, wanda hakan ya saba da hukuncin kotun Jihar Oyo da ta ba jam’iyyar damar ci gaba da shirinta. 

 

Da yake martani, Abdullahi ya ce PDP ba za ta sake bari “hukuncin da aka siya”A cewarsa ya dakile ta ba, yana mai jaddada cewa jam’iyyar ta PDP ta samo asali daga ‘yan Najeriya, ba daga kotu ba

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!