Labarai
Jam’iyyar PDP a jihar Jigawa ta nemi uwar jam’iyyar ta kasa da ta janye dakatarwar da aka yi wa Sule Lamido

Jam’iyyar PDP reshen Jihar Jigawa ta nemi shugabancin jam’iyyar na ƙasa da ya gaggauta janye dakatarwar da aka yi wa tsohon gwamnan jihar, Sule Lamido, daga Kwamitin Amintattu na jam’iyyar.
Hakan dai na cikin wata sanarwar da Shugaban jam’iyyar na Jihar, Dakta Babandi Ibrahim Gumel, ya fitar a ranar Asabar 20 ga Disambar da muke ciki.
Sanarwar ta bayyana dakatarwar a matsayin rashin adalci, tana mai cewa neman hakki ta hanyar doka bai zama dalilin yin wannan hukunci ba, tare da jaddada cewa matakin ya saba da kundin tsarin mulkin jamʼiyyar.
Jam’iyyar PDPn ta yi kira ga uwar jam’iyyar ta kasa da ta gyara wannan mataki domin tabbatar da haɗin kai da dimokuraɗiyyar a cikin jam’iyyar.
You must be logged in to post a comment Login