Labarai
Jam’iyyar SDP ta kori El-Rufai daga zama a cikinta

Jam’iyyar SDP ta kori tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir el-Rufai, inda ta bayyana cewa ba zai iya shiga jam’iyyar ba a kowane matsayi na tsawon shekaru 30 masu zuwa.
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran SDP na ƙasa Araba Aiyenigba ya fitar a Abuja, jam’iyyar ta ce, El-Rufai bai taɓa yin rajista da jam’iyyar ba a hukumance ba a matakin mazaɓa kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada.
Aiyenigba ya ce, duk da haka, tsohon gwamnan ya fito fili ya yi ikirarin zama memba a shafukan sada zumunta da kuma “takardun jabu” don goyon bayan ikirarin nasa.
Jam’iyyar ta kuma yi zargin cewa ya haɗa kai da jam’iyyar ADC tare da neman janyo jam’iyyar SDP cikin kawancen siyasa mara izini.
SDP ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta INEC da sauran hukumomin da abun ya shafa da kada su amince da El-Rufai a matsayin mamba.
Jam’iyyar SDP ta ce, tsohon gwamnan na Kaduna ba shi da hurumin wakilci ko yin magana a jam’iyyar.
You must be logged in to post a comment Login