Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Jigawa

Jana’izar Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi

Published

on

Da misalin karfe biyu na ranar yau Laraba ne ake sa ran za a yi jana’aizar marigayi sarkin Dutse Alhaji Dakta Nuhu Muhammad Sanusi wanda ya rasu a yammacin jiya Talata bayan gajeriyar rashin lafiya.

Za dai a yi jana’izar ta sa ne a babban masallacin idi na birnin Dutsen jihar Jigawa.

Wakilin freedom Radio ya rawaito cewa kafin rasuwarsa marigayi Alhaji Dakta Nuhu Muhammad Sanusi, ‘ya bayar da umarnin da idan ya mutu a binne shi a cikin mutane, sabanin yadda akeyiwa sarakuna’.

Yanzu haka dai gidan na cike da manyan-manyan baki daga wurare daban-daban, kama daga sarakuna, ciki kuwa harda mai alfarma Sarkin Musulmai Alhaji Sa’ad Abubakar na III, da kuma Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, dama wasu da dama, dama masu mukaman gawmnati wadanda suke jiran lokacin jana’izar tasa.

Rahoton: Umar Aminu Shuwajo

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!