Kowane Gauta
Janye yajin aikin da NLC ta yi, ya sabawa kundin tsarin mulkin ta – tsohon shugaban NLC
Tsohon shugaban kunguyar Kwadago ta kasa kwamared Isa Tijjani yace janye yunkurin kungiyar kwadago ta kasa da suka yi baya bisa ka’ida kuma ya sabawa kundin tsarin mulkin kungiyar baki daya.
Kwamared Isa Tijjani ya bayyana hakan ne ta cikin shirin kowane Gauta na Freedom Radio.
Isa Tijjani ya kara da cewa janye yajin aiki da kungiyar ta yi ya nuna karara cewa talakawa zasu yanke tsammani daga kungiyar kasancewar alkawarin da gwamnatin tarayya tayi bazata iya cika shi ba.
Kwamared Tijjani yace janye yajin aikin da kungiyar ta yi ya nuna cewa akwai ayar tambaya akan kamarin domin wadanda lamarin ya dama matuka ba zasu kara yadda da kungiyar ba.
You must be logged in to post a comment Login