Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jaruma Amal Umar ta nemi Kotu ta hana ƴan sanda cafke ta

Published

on

Jarumar Kannywood Amal Umar ta nemi Kotu ta hana mataimakin sufeton ƴan sanda mai kula da shiyya ta ɗaya da Kwamishinan ƴan sandan Kano da wani ɗan sanda mai bincike kamata.

Amal ta shigar da ƙorafinta a kotun jiha mai lamba 17 da ke Miller Road a Kano, inda ta ke neman a dakatar da ƴan sandan daga yunƙurin sake kamata.

Rahotonni sun ce ƴan sandan sun nemi Amal ne bisa zargin damfara da ake yiwa saurayinta mai suna Ramadan.

Wani mai suna Alhaji Yusuf Adamu ne yi ƙorafi ga ƴan sandan bisa zargin Ramadan ya karɓi kuɗi har miliyan arba’in a hannunsa da zummar kasuwancin sayar da wayoyi.

Bayan da ƴan sanda suka kamar Ramadan tare da soma bincike sai ya ce, ya siyawa Amal ɗin Mota, sannan ya kama mata shago ya zuba mata kaya na miliyan biyar.

Ya ce, ya kuma bata miliyan uku domin ta biya wa mahaifinta wasu kuɗaɗe ake binsa.

Ya kuma bata wasu kuɗaɗen daban ta hanyar transfer.

Hakan ne ya sanya ƴan sanda suka cafke jaruma Amal Umar, tare da karɓe motar, sannan kuma suka ci gaba da bincikarta, abin da ya sa ta garzaya kotu.

Yayin zaman kotun na ranar Alhamis, Barista Yusuf Dan Sulaiman lauyan Alhaji Yusuf Adamu ya nemi a sanya su a cikin wanda ake ƙara.

A nan mai shari’a Sunusi Ado Ma’aji ya sanya ranar 16 ga watan Disamba mai kamawa domin duba buƙatar lauyan.

Bayan fitowa daga Kotun Freedom Radio ta so jin ta bakin lauyar Amal Umar wato Barista Adama Usman, amma ta ce ba za ce komai a lokacin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!