Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jaruma ZPreety ta caccaki ‘yan soshiyal midiya

Published

on

Matashiyar jarumar fina-finan hausa  Zulihat Ibrahim wacce aka fi sani da ZPreety ta caccaki masu amfani da kafafan sada zumunta wadanda ake kira da ‘yan soshiyal midiya.

Cikin wani faifan bidiyo da jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram ta yi suka kan wadanda tace suna bibiyar al’amuran ta, da na sauran jarumai inda da zarar sun wallafa wani hoto ko bidiyo sai su dauka suje su wallafa shi ta wata fuska ta daban.

Jaruman Kannywood sun fara bayyana da Iphone 11

Jarumar ta yi kakkausan kalamai na musamman ga masu wallafa bayanai a dandalin YouTube inda ta ce mafi yawan su basu da aikin yi face su shirya karya da gulma don su bata jaruman masana’antar Kannywood a idon duniya.

 

ZPreety ta yi wata barazana inda ta ce “ Ku kiyaye ni zan fa iya yin wani abu akan duk wanda ta samu yana bibiyarta ta irin wannan sigar”

Kawo yanzu dai sama da mutane dubu biyu ne dai suka kalli wannnan bidiyo na jarumar a shafinta yayin da sama da mutum dari suka yi tsokaci akai.

Mafi yawan mabiyan jarumar da suka yi tsokaci akan labarin dai sun rika bata hakuri akai.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!