Connect with us

KannyWood

Jaruman Kannywood sun fara bayyana da Iphone 11

Published

on

Watanni biyu bayan fitowar Iphone 11 kasuwa, fitacciyar jarumar Kannywood Rahama Sadau itace jaruma ta farko da aka gano ta a kasar Dudai rike da dalleliyar wayar hannu ta zamani kirar Iphone 11.

Jaruman Kannywood dai sun shahara wajen nuna irin wayoyin da suke rikewa.

Ita dai wannan waya akalla tana kaiwa fiye da rabin miliyan.

A ranar 20 ga watan satumba ne dai wayar Iphone 11 ta shiga kasuwa.

Continue Reading

KannyWood

Ban dauki “selfie” da gawar mahaifina ba -Hafsat Idris

Published

on

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausar nan Hafsat Idris wadda akafi sani da Barauniya ta musanta rade-radin da ake ta yadawa a kafafan sada zumunta na cewa ta dauki hoton dauki da kanka wato “selfie” da gawar mahaifinta.

A safiyar yau ne dai aka tashi da labarin mutuwar mahaifin jarumar kamar yadda ta wallafa a shafinta na Instagram hade da wani hoto tare da mahaifin nata a lokacin da yake fama da rashin lafiya.

Sai dai wasu al’umma sunyi mata mummunar fahimta inda suka rika cewa jarumar ta dauki hoton ne bayan da mahaifin nata ya rasu.

Sai dai a yammacin yau jaruma Hafsat Idris ta musanta zargin inda ta sake wallafawa a shafinta cewa “nayi posting hoto tare da mahafina wasu na cewa wai nayi hoto da gawa, ya za’ayi hoto da gawa? Banyi hoto da gawa ba. Wannan hoton tun da rayuwarshi muka dauka.
Allah ya mishi rahma ameen”.

Wannan dai ya kawo karshen cecekucen da akeyi kan wannan batu.

Allah ya kyauta, ya kuma jikan musulmi baki daya.

Continue Reading

KannyWood

Mu masu gyaran tarbiyya ne –Teema Makamashi

Published

on

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausar nan Teema Makamashi ta karyata rade-radin da ake yadawa na cewa jaruman masana’antar Kannywood basu da tarbiyya.

Yayin wata tattaunawa da jarumar tayi da Freedom Radio ta bayyana cewa “Mu muke da tarbiya, saboda mu muke bada gudummuwa wajen gina tarbiyar ‘ya’yan mutane, na san wadanda suke yawace-yawacen sata, da karuwanci amma sanadiyar wani film da suka kalla sun daina”.

Teema Makamashi ta kara da cewa mafi yawa bakin haure a masana’antar ne ke bata musu suna, amma su ‘yan film mutane ne masu daraja da tarbiyya.

Sannan jaruma Teema Makamashi ta ja hankalin jaruman masana’antar Kannywood kan su daina yiwa juna hassada domin hakan na daya daga dalilan dake kawo cikas ga cigaban masana’antar.

Rubutu masu alaka:

‘Yan film sun karrama kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano

Ina so na zama ‘yar kasuwa kamar Dangote –Sadiya Kabala

A shirye nake na auri Kamaye a zahiri –inji Adama

Continue Reading

KannyWood

A shirye nake na auri Kamaye a zahiri –inji Adama

Published

on

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausar nan Zahra’u Saleh wadda akafi sani da Adama matar Kamaye acikin wasan kwaikwayon nan na Dadin Kowa ta bayyana cewa a shirye take da ta auri abokin karawarta a wasan kwaikwayon wato Dan’azimi Baba Chediyar ‘Yan Gurasa wanda akafi sani da Kamaye.

A yayin wata tattaunawa da Freedom Radio tayi da jarumar a jiya Laraba Adama ta bayyana cewa “shi aure al’amari ne na Allah, kuma idan Allah ya rubuta cewa Kamaye mijina ne to hakika sai na aureshi, kuma ba abin mamaki bane domin kuwa a shirye nake da na aureshi”

Jaruma Adama ta kara da cewa ita sam ba mafadaciya bace a zahiri, kawai dai wasa ne aka bata tsarin ta fito a matsayin mafadaciya, a karshe tayi kira ga sauran jaruman masana’antar Kannywood da su taimaka su hada kansu su kaucewa rikice-rikice domin tabbatar da zaman lafiya da cigaba ga jaruman da masana’antar su.

Labarai masu alaka:

‘Yan film sun karrama kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano

Ina so na zama ‘yar kasuwa kamar Dangote –Sadiya Kabala

Continue Reading

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.