Labarai
Jega ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta daina naɗa ƴan siyasa marasa kwarewa a muƙamai

Tsohon shugaban hukumar zaɓe ta Najeriya INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta daina nada ’yan siyasa marasa kwarewa da mutanen da ba su da cancanta domin shugabantar jami’o’in kasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Farfesa Jega na cewa, ana buƙatar shugabannin da suka dace, masu hangen nesa da kwarewa, ba masu neman ramko ko lada a siyasa ba.
Ya kuma ce tsoma bakin yan siyasa wajen nada Vice Chancellors, shugabannin gudanarwa, da sauran manyan mukamai ne ya janyo durkushewar gudanarwa da tabarbarewar ingancin ilimi.
You must be logged in to post a comment Login