Jigawa
Jigawa: Ƴan sanda sun cafke matasa 21 da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi

Rundunar ƴan sanda jihar Jigawa ta sanar da cafke mutane 21 da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a wurare daban-daban na jihar.
Haka kuma, rundunar ta ce, ta kwace kwayoyi iri-iri ciki har da Tramadol da Exol da D5 da kuma kuɗin da ake zargin kudin sayar da kwayoyi ne.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ta Jigawa SP Shiisu Lawan Adam, ne ya bayyana haka ta cikin wani saƙon Murya da ya aiko wa Freedom Radio.
Haka kuma Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Dahiru Muhammad, ya yaba wa jami’an tsaron bisa jajircewa tare da yin kira ga jama’a da su ci gaba da ba da sahihan bayanai domin tabbatar da tsaro.
You must be logged in to post a comment Login