Jigawa
Jigawa: Ƴan sanda sun cafke matasan da ake zargi da safarar ƙwayoyi

Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa, ta samu nasarar kama wasu bata-gari da ake zargin su da safarar miyagun kwayoyi a kananan hukumomin Mai Gatari da Garki da kuma garin Fagam, a yayin wani samame da rundunar ta gudanar a baya bayan nan.
Mai magana da yawun rundunar, SP Shisu Lawan Adam, ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai, inda ya bayyana cewa rundunar na ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
SP Shisu Lawan Adam, ya kuma ce da zarar an kammala bincike, za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu domin su fuskanci hukuncin da ya dace da su.
You must be logged in to post a comment Login