Labarai
Jigawa: Ƴan sanda sun cafke mutane 13 da ake zargi da safarar ƙwayoyi

Rundunar ‘Yan Sanda jihar Jigawa ta cafke mutane 13 da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a samamen da ta gudanar a baya bayan nan.
A cewar mai magana da yawun rundunar, SP Shisu Lawan Adam, an kwato exol da tramadol sai D5 sama da dubu biyu,da kuma wiwi da sauran ƙwayoyi, tare da wayoyi.
SP Shisu Lawan ya kuma ce tune aka gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu bayan bincike domin su fuskance hukunci, yayin da Kwamishinan ‘Yan sanda na jihar, Dahiru Muhammad, ya ja kunnen masu aikata laifuka da su daina, tare da kira ga al’umma da su rika bayar da sahihan bayanai domin tabbatar da tsaro.
You must be logged in to post a comment Login