Connect with us

Labarai

Jigawa: Hukumar PCACC ta kwato fiye da Naira miliyan 200 tare da warware kusan korafi 200

Published

on

Hukumar karbar korafi da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Jigawa, ta kwato kudi sama da Naira miliyan 200 tare da warware korafe-korafe kusan 200 daga cikin guda 300 da al’ummar jihar suka shigar cikin watanni 16 da kafata.

 

Jami’in hulda da Jama’a na hukumar Yusuf Sulaiman ne ya bayyana haka ga Freedom Radio a madadin hukumar karkashin jagorancin Barr Salisu Abdu.

 

Haka kuma, ya kara da cewa hukumar ta samu nasarorin ne ta hanyar bibiya da gayyato wadan da aka shigar da korafi kan su, da suka hada da jami’an gwamnati zuwa daidaikun mutane a sassan jihar.

 

Ya kuma bukaci al’umma da su rika bewa hukumar hadin kai ta hanyar taimaka mata da sahihan bayanan danne hakki ko zamba da sauran korafe-korafe.

 

A watan biyu na shekarar 2024 ne gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya kirkiro hukumar da nufin kakkabe aiyukan cin hanci da rashawa a gwamnatance, tare da karbar korafin mutane kan abin da ya shafi hakki da dai sauran su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!