Labarai
Jigawa: Yan sanda sun cafke wadanda ake zargi da satar mota da Sojan gona

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, ta kama wani mutum da ya ke yin ƙarya da cewa shi soja ne tare da wasu matasa biyu da ake zargi da satar mota a Kafin Hausa.
An cafke su ne bayan sun yi hatsari da motar da ake zargin ta satace, daga bisani kuma aka gano ɗaya daga cikinsu, Kabiru Musa, ba soja ba ne.
Bayan kama sojan bogen, an same shi da katunan cirar kudi na ATM guda bakwai da lasisin tuki guda biyu da wasu abubuwa da ake zargin ana amfani da su wajen zamba.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar ta Jigawa SP Lawan Shiisu Adam, nre ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Dutse babban birnin jihar.
A nasa bangaren, wanda ake zargi da aikata laifin Kabir Musa mazaunin Unguwa Rimin Kebe da ke Karamar Hukumar Ungogo a Kano, ya amsa cewa tabbas shi sojan gona ne tare da bayyana yadda aka cafke shi.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Dahiru Muhammad, ya yaba da ƙoƙarin jami’an rundunar tare da jaddada aniyarsu ta tabbatar da tsaro, kana ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba da sahihan bayanai da za su rika taimaka wa jami’an tsaro wajen kama bata gari.
You must be logged in to post a comment Login