Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jihar Kano ta sami sabon kwamishinan ‘yan sanda

Published

on

Babban sefeton ‘yan sanda na kasa Mohammed Adamu ya aike da sababin kwamishinoni ‘yan sanda zuwa jihohi bakwai biyo bayan daga linkafar wasu daga cikin kwamishinonin ‘yan sanda zuwa mataimakan babban sefeton ‘yan sanda na kasa.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da mai Magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta kasa Frank Mba ya fitar cewa nadin zai fara aiki ne nan take.

Sanawar ta ce CP Habu Sani Amadu shi ne sabon kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano  sai CP Lawal Jimeta da zai zama kwamishinan ‘yan sanda na jihar Edo da CP Philip Sule Maku wanda yanzu shi ne sabon kwamishinan ‘yan sanda na jihar Bauchi da CP Nkereuwem A. Akpan shi ne sabon kwamishinan ‘yan sanda na jihar River da CP Kenneth Ebrimson wanda zai zama sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar Akwa Ibom da kuma Imohimi Edgal shi ne zama aiki a matsayin sabon kwamshinan ‘yan sanda na jihar Ogun.

Haka zalika sanarwar ta kara da cewar mai rikon mukamin kwamishinan ‘yan sanda na jihar Lagos CP Odumosu H. Olusegun shi ne zai kasance kwamishinan ‘yan sanda na dai jihar Lagos.

Rundunar ‘yan sandar jihar Kano ta sake ceto wani yaro a Anambra

Ana zargi alkali da baiwa ‘yan sanda satar amsa

‘Yan sanda sun cafke sojoji kan KAROTA

Babban sefeton ‘yan sandan ya bukaci sababbin kwamishinonin da su hada kai da tsofafin kwamishinonin da su ka gada don tabbatar da sun inganta ayyukan su waje kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Muhammad Adamu ya kuma umarci sababbin kwamishinonin da su yi aiki da masu ruwa da tsaki wajen bunkasa ayyukan su da kuma amfani da hanyoyin yake da ta’addaci.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!