Connect with us

Labaran Kano

An cafke budurwa na yunkurin shigar da kwaya gidan Kurkukun Kurmawa na Kano

Published

on

Hukumomin gidan gyaran hali na Kurmawa dake nan Kano sun kama wata Budurwa mai suna Zainab Musa da yunkurin shigar da kwaya gidan.

Zainab Musa mai kimanin shekaru Ashirin dake unguwar Hotoro Dan Marke a nan Kano, jami’an sun kama to ne da yammacin yau Alhamis dai-dai lokacin da ta je gidan.

Ka zalika hukumomin gidan suna zargin Zainab Musa da kokarin shigar da kwaya samfurin Exol har guda 360 acikin miya zuwa gidan gyaran halin na Kurmawa.

Wakilin mu Abubakar Sabo ya gana da budurwar bayan da aka kamata yayin ta bayyana cewa ita bata san menene a ciki ba

Hukumomin dai sun kama Zainab da kwayar 360, Tana mai cewa ta zo gidan gyaran halin ne domin kawo wa dan uwanta abinci.

Saidai wani abokin dan uwan nata Mai suna Abdullahi mazaunin unguwar Hotoro, ya ba ta wannan kwanon don ta taho dashi, amma bata san menene aciki ba.

Kakakin hukumar gidan gyaran halin na jihar Kano DSP Musbahu Lawan Kofar Nassarawa ya tabbatar da afkuwar Al’amarin yana mai cewa yanzu haka wannan budurwa tana hannunsu kuma zasu fadada bincike daga bisani su mikata ga rundunar ‘yan sanda.

Rubutu masu nasaba:

Kun san dalilan da suka sanya aka garkame Sadiya Haruna a gidan yari?

Za’a koyar da fursunoni arba’in karatun Firamare

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 332,987 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!