Connect with us

Labaran Kano

Rundunar ‘yan sandar jihar Kano ta sake ceto wani yaro a Anambra

Published

on

Rundunar ‘yan sandar jihar Kano ta ceto wani yaro dan shekara 11 da aka sace daga unguwar PRP  da ke unguwar brigade a nan Kano, a shekara ta 2014 aka kuma sayar da shi a jihar Anambra.

Kakakin rundunar ta ‘yan sanda DSP Abdullahi Haruna ya ce  Paul Onwe da Mercy Paul ne suka  sace tare da sayar da yaron  mai suna Muhammad Ya’u, a kan kudi naira dubu dari biyu.

Ya kara da cewa  tuni aka mayar da Muhammad Ya’u addinin Krista aka kuma canza masa suna Chinedu Ogbodo daga hannun wadanda suka saye shi.

Rahotannai na nuni da cewar tuni aka kama wadanda ake zargin da sace yaro su uku, inda kuma yanzu haka suke karkashin binciken ‘yan sandabinciken ‘yan sanda , biyo bayan yara tara da aka ceto a yan kwanakin nan.

DSP Haruna ya ce rundunar na iya kokarinta wajen ceto yara yan Kano da aka sace tare da sayar da su a jihar ta Anambra

Labaran Kano

Rundunar ‘yan sanda ta Kano ta ja hankali alumma kan zaben ranar Asabar

Published

on

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano karkashin jagorancin Kwamishinanta Cp Habu A. Sani, na sanar da al’ummar Jihar Kano cewa, hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC zata sake gudanar da zabuka Ranar Asabar 25/01/2020 a Kananan hukumomin Bebeji, Tudun Wada, Doguwa, Rogo, Kumbotso, Kiru, Bunkure, Minjibir da kuma Karamar Hukumar Madobi.

Hukumar na bada tabbacin cewa tayi hadin kai da takwarorin hukumomin tsaro dake nan Kano domin tabbatar da anyi zabe lafiya an kuma gama lafiya,

A don haka, al’umma su tabbata sun kiyaye da wasu daga cikin sharudan da ta gidanya don samun nasarar zaben da suka hadar da,duk wani motsin ababen hawa kamar Motoci, Adaidaita Sahu da Babura an haramta shi tun daga daren jajiberen ranar zaben har a kammala a wadannan kananan Hukumomi Guda Tara da za’ayi zabe,  in banda motocin Asibiti, Jami’an Kashe Gobara, Ma’aikatan zabe da wadanda hukumar zaben ta tantance.

Haka zalika rundunar bata yarda duk wasu matasa yan tada zaune tsaye su kusanci inda ake gudanar da zaben ba.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da kakkin rundunar ‘yan sand ana jihar DSP Abdullahi Haruna ya sanyawa hannu cewa, ta hana  daukar duk wani makami ko kuma abun cutarwa a yayin gudanar da zaben, jami’an tsaro ba za su amince da haka ba.

Haka kuma  Iya wadanda suka cancanci zabe za’a bari a harabar zaben.

Bugu da kari da duk wanda bashi da katin zabe da yake nuna lambar akwatin zabensa a wannan  yanki, hukuma zatayi awon gaba dashi.

Dangane da haka rundunar bata aminta da kawo wani mutum ko wasu mutane inda ake zaben ba. Matukar ba hukumar INEC ce ta tantance suba sannan  iya wakilan Jam’iyyun da hukumar zabe ta tantance aka amince da zuwan su zaben.

Daga karshe  rundunar ‘Yan sanda ta Jihar Kano na yiwa al’umma fatan yin zabe lafiya kuma a gama lafiya.

A Don neman taimakon  gaggawa ko kuma sanar da faruwar wani lamari, sai a kira wadannan lambobin 08032419754, 09029292926, 08123821575.

Continue Reading

Labaran Kano

Zamu gina Asibitoci a sabbin masarautu 4 na Kano- Ganduje

Published

on

Gwamnatin jihar Kano tace tuni ta bayarda kwangilar gina Asibitoci a dukkannin sabbin masarautin jihar Kano hudu wadanda zasuci gadaje dari hudu domin bunkasa harkar lafiya a jihar Kano.

Sakataren gwamnatin Kano Alhaji Usman Alhaji ne ya bayyana hakan a yayin taron Kungiyar Likitocin kananan yara ta kasa NAPCON.

Alhaji Usman Alhaji yace banda gwamnatin jihar Kano babu wata jiha a fadin Najeria data warewa bangaren lafiya kaso mafi yawa acikin kasafin kudinta sai jihar Kano.

Sakataren gwamnatin jihar Kano Usman Alhaji ya kuma nanata cewa gwamnatin jihar Kano zata cigaba da bunkasa harkar lafiya domin ciyarda bangaren lafiya gaba.

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito cewa Sakataren gwamnatin Kano Usman Alhaji na cewa gwamnatin Kano zata cigaba da baiwa bangarorin ilimi da lafiya fifiko sama da komai kamar yadda Majalisar dinkin duniya ta shaida cewa duk kasar dake son cigaba dole ne sai ta fifita wadannan bangarori guda biyu

Continue Reading

Labaran Kano

Tsohuwar budurwar angon Ba’amurkiya wani saurayi zai kai ta Saudiyya

Published

on

Har yanzu labarin matashin nan Suleiman Baba Yaro da ya tsinci dami a kala bayan soyayyar social media, da ta zame masa sanadin kulla alakar I love U da baturiya ba ta lafa ba, koda ya ke ta manyanta amma kowa ya yi ittifakin cewar, wannan ba matsala bane.

To amma yanzu tsohuwar budurwarsa Nafisa Tahir wacce a baya mun kawo muku hira da ita da take cewar, tayi tawakalli kuma Umma-ta-gai-da-Aisha.

Sai dai wancan hira da mu ka yi da ita ya jawo mata wani farin jini daga masoya inda mutane daga sassan kasar nan daban- daban ke cewar, su fa ta yi musu su na ciki, wasu cewa su ka yi ganin hoton ta ne ya ba su kwarin gwiwa domin sun ce duk inda kyau ya kai Nafisan ta kai.

Yayin da wasu ke cewar, muryar ta kawai da su ka ji ta burge su, yayin da wasu ke cewar ai abin da ya faru kuma su ka jiyo ta ta na tawakalli shi ne ya birge su su ka ga da cewar yi ma ta na huce, to amma ko da muka tuntube ta dan jin ko cikin tarin wadannan manema za ta zaba ta darje?

Nafisa ta ce lallai, ta dai gode amma ba wannan ne a gabanta ba, shi dai aure ikon Allah ne kawai a cigaba da addua.

Wakilinmu Aminu Abdu Bakanoma ya zanta da guda daga cikin mutanen da su ka nemi a sada su da Nafisa domin gwada sa’arsu, wanda ya ce, shi a shirye ya ke kuma daga auren sai tafiya Hajji.

Continue Reading

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!