Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Jihar Kwara ce za ta karbi bakuncin gasar wasanni ta kasa a shekarar 2022 -Abdurrahman Abdurrazaq

Published

on

Gwamnatin jihar Kwara ta ce itace za ta karbi bakuncin gasar wasanni ta kasa a shekara mai kamawa ta 2022.

Gwamnan jihar AbdulRahman AbdulRazaq ne ya bayyana hakan a ranar Talata 19 ga watan Oktoban 2021 a garin Ilorin jihar, yayin rufe gasar wasanni ta matasa ‘yan kasa da shekaru 15 da aka gudanar a jihar.

AbdulRazaq ya kuma tabbatar da cewa dukkan wasu shirye-shirye da suka kamata a yi yayin gudanar da gasar tuni jihar tasa ta Tanadesu.

Gasar da aka gudanar a jihar ta Kwara itace karo ta 6 da ake gudanarwa a kasar nan, inda ake gudanar da wasanni daban-daban tsakanin matasan kasar.

Jihar ta Kwara dai yayin gasar ta kare a matsayin ta 6 daga cikin jihohin kasar nan da suka halarci gasar.

Ta kuma samu damar lashe kyautar sarkar Zinare 10 da ta Azurfa itama 10 sai kuma Tagulla guda 12.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!