Labarai
Jihohi sun kashe sama da Naira biliyan 525 kan matsalar tsaro

Akalla jihohin kasar nan sun ware jimillar Naira biliyan Sama 525 a matsayin kuɗaɗen da za’a yi amfani da su wajen kula da harkokin tsaro tsakanin shekarar 2023 zuwa 2025, sai dai duk da haka hare-haren ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da kashe-kashe na ci gaba da ƙaruwa.
Ta cikin wani rahoto da jaridar PUNCH ta wallafa ya nuna cewa jihar Borno ta fi kowa kashe kudi da ya kai Biliyan sama da 57 sai Anambra mai 42.57 Delta mai biye mata baya da Naira 38.44 da kuma Benue ta ka kashe Naira 36.87 sauran jihohin kuma sun fitar da ƙananan alkaluma, yayin da Gombe, Kebbi, Niger da Yobe ba su fayyace bayanan su ba.
Masana da ƙungiyoyin kwadago na cigaba da sukar wannan shiri na kashe kudade ba tare da samun cigaba a fannnin na tsaro ba.
A dai-dai lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya jaddada muhimmancin ƙarfafa ƙananan hukumomi da tsaron al’umma wato community policing domin dakile matsalar.
You must be logged in to post a comment Login