Connect with us

Labarai

Kai tsaye: Ganduje ya kammala gabatar da kasafin kudin 2020

Published

on

Gwamnan Ganduje ya kammala gabatar da kunshin kasafin kudin badi a gaban majalisar dokoki ta jihar Kano.

Dr, Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar da daftarin kasafin kudin  badi  ya kama za’a kashe fiye da Naira biliyan dari da casa’in  a shekara kudi mai kamawa.

Ganduje ya kara da cewaer za’a kashewa sabuwar  ma’aikatar Adini fiye da Naira miliyan dari shida  yayin da kuma za’a  kashewa ma’aikatar yawon bude idanu  fiye da Naira miliyan dari wajen bunkasa ayyukan ta.

Yayin da kuma  gwamnati ta kashe miliyoyin kudi wajen gina karin  masarautun yanka da ta kirkro

Taken daftarin kasafin kudin badi shi ne “kasafin kudi mai dorewa don cigaban alumma”

Har ila yau, Gwaman Ganduje ya yabawa jami’an tsaro saboda kokarin da suka yi na kwato yaran Kano 9 da aka sace aka kai jihar Anmabra, kuma lamuran tsaro sun inganta a jihar nan.

Dr, Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar da daftarin kasafin kudin  badi  ya kama za’a kashe fiye da Naira biliyan dari da casa’in  a shekara kudi mai kamawa.

Ganduje ya kara da cewaer za’a kashewa sabuwar  ma’aikatar Adini fiye da Naira miliyan dari shida  yayin da kuma za’a  kashewa ma’aikatar yawon bude idanu  fiye da Naira miliyan dari wajen bunkasa ayyukan ta.

Yayin da kuma  gwamnati ta kashe miliyoyin kudi wajen gina karin  masarautun yanka da ta kirkro

Taken daftarin kasafin kudin badi shi ne “kasafin kudi mai dorewa don cigaban alumma”

Har ila yau, Gwaman Ganduje ya yabawa jami’an tsaro saboda kokarin da suka yi na kwato yaran Kano 9 da aka sace aka kai jihar Anmabra, kuma lamuran tsaro sun inganta a jihar nan.

A halin da ake cikin gwamnan Abdullahi Umar Ganduje ya sauya harshe zuwa harshen hausa yana mai cewa ya zama wajibi ya bayyana yadda kushin daftarin kasafin kudin cikin harshen Hausa.

Ka zalika  Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje na gabatar da kunshin kasafin kudin badi wanda ya kai naira biliyan dari da casain da bakwai da miliyan Dari shida da tamanin da Uku da dubu Dari Uku da hamsin da Uku da Dari shida da hamsin da Tara.

A cewar gwamnan za a yi amfani da kudaden wajen gudanar ayyukan raya kasa a fadin jihar Kano a shekara mai zuwa.

Gwamna Ganduje ya ce bangaren manyan ayyuka zai samu jimillan naira biliyan Dari da goma sha bakwai da miliyan Dari bakwai da goma da dubu Dari shida da ashirin da shida da Dari takwas da tamanin da daya.

A cewar gwamnan na Kano ayyukan yau da kullum za su samu naira biliyan sabain da Tara da miliyan Dari Tara da sabain da biyu da dubu Dari bakwai da ashirin da shida da Dari bakwai da sabain da takwas.
Ya ce kasafin kudin mai taken: Dorewar bunkasar ci gaban alumma zai tai maka gaya wajen bunkasa tattalin arzikin jihar Kano.

Gwamnan na Kano ya kuma ce maaikatar lafiya za a kashe sama da kaso goma sha biyar na kasafin kudin wajen kyautata kiwon lafiyar alummar jihar.

Wakilin mu na majalisar dokokin Kano ya ruwaito cewa harkar samar da ruwan sha zai lakume sama da naira biliyan goma sha biyar.

Gwamnan Dr, Abdullahi Umar Ganduje ya fara jawabin kan irin cibagan da ya aka samu a shekarar da ta gabata cikin kunshin kasafin kudin wannan shekarar.

Yana mai cewa gwamnatin sa ta sami nasarar aiwatar da manyan ayyuka daga cikin kasafin kudin da aka gebewa wannan shekarar.

Ya ce cikin idan aka yi nazari cikin kasafin kudin na wannan shekara kan harkokin kasuwanci da ma’adinai an sami cigaba mai ma’an

Kazalika Gwamnan Ganduje ya kara da cewar an daga linkafar wasu asibitocin don inganta kiwon lafiya a jihar nan.

wamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya isa majalisar dokoki don gabatar da daftarin kudirin kasafin kudin badi.

Gwamnan Dr, Abdullahi Umar Ganduje ya isa harabar majalisar dokoki da misalin karfe goma da kwata.

Ganduje dai ya fara jawabi da harshen Turanci.

Abunda ya kamata ku sani kan kasafin kudin badi

Majalisa:An samu hargitsi yayi gabatar da kunshen kasafin kudin bad

Coronavirus

Nijar: An fara feshin magani kan Corona a makarantu

Published

on

Hukumomin a jahar Damagaram sun kaddamar da fara feshin maganin rigakafin Covid-19 a cikin makarantun boko

A sadiyar Litinin dinnan ne shugaban kwamitin yaki da wannan cuta kuma magatakardar fadar gwamnan jihar Damagaram ya jagoranci bikin kaddamar da feshin a cikin makarantar Mela Douaram da ke tsakiyar birnin na Damagaram.

Magatakardar ya bayyana cewa sun fara wannan aiki ne a wani mataki na kare daliban daga kamuwa da wannan cuta ta Covid-19.

Wakilin mu Yakubu Umar Mai Gizawa ya rawaito mana cewa tun a kwanakin baya ne dai gwamnati ta sanar da ranar daya ga watan Yuni mai zuwa a matsayin ranar ranar da za’a koma bakin ajijuwan makarantun bayan shafe tsawan lokaci suna rufe sakamakon yaki da ake da cutar Covid-19.

Labarai masu alaka:

Amsoshin tambayoyi 20 kan cutar Corona – Dr. Ibrahim Musa

Covid-19: Gwamnati ta bada damar cigaba da sufuri a Nijar

Continue Reading

Coronavirus

Covid-19: Babu hawan sallah a Kano

Published

on

Maimartaba Sarkin Alhaji Aminu Ado Bayero yayi kira ga al’ummar Kano da su kiyaye dangane da yanayin da ake ciki na annobar Covid-19 da ta janyo sauyawar al’adun fada.

Sarkin ya bayyana hakanne a daren Asabar a Kofar Kwaru yayin da yake jawabi a gaban manyan hakiman sa kan yadda za a gudanar da sallar bana.

Maimartaba Aminu Ado ya ce babu hawan sallah na al’ada da masarautar Kano ta sabayi duk shekara saboda yanayin Corona.

Sarkin ya kara da cewa maimakon hakan Sarki zai tafi idi a kafa, inda zai fito ta kofar Fatalwa har zuwa filin idi na Kofar Mata da safe.

Bayan an idar da sallar idi kuma Sarkin zai biyo ta unguwar Kofar Wambai da Zage, sannan ya biyo ta Dorayi da Shahuci daga nan ya zarto zuwa Kofar Kwaru a Mota.

Ana sa ran Sarkin zai yi jawabi ga al’ummar Kano bayan sakkowa daga sallar idin a Kofar Kwarun kamar yadda al’adar masarautar Kano take.

Wakilinmu na fadar sarkin Kano Muhammad Harisu Kofar Nassarawa ya rawaito mana cewa Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya jajantawa al’ummar Kano sakamakon rashe-rashen da aka samu sannan yayi fatan marasa lafiya Allah ya basu lafiya.

A karshe Sarkin yayi kira ga al’ummar Kano da su cigaba da kiyayewa tare da yin biyayya ga matakan da masana kiwon lafiya suka sanya wajen dakile yaduwar cutar Corona.

A shekarun baya dai, kafin annobar Covid-19 ta bullo akan shafe kwanaki biyar ana gudanar da hidimomin al’ada na masarautar Kano a yayin bikin karamar sallah.

Hoton Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero.

Continue Reading

Labarai

Ana shagulgulan karamar sallah yau a Nijar

Published

on

Al’ummar jamhuriyar Nijar sun bi sahun takwarorin su daga kasashen musulman duniya wajen shagulgulan salla karama.

A jiya ne dai majalisar musulunci ta kasar ta fitar da sanarwar ganin jinjirin watan a wasu sassan kasar wanda hakan ke nufin kawo karshen watan azumin Ramadan.

Tun da sanyin safiya ne dai al’ummar musulmin kasar suka yi fitar dango dan halartar masallatan idi.

Da misalin karfe 9 na safe ne, Limamin babban masalacin Idi ya jagoranci sallah raka’a biyu kamar yadda addinin musulunci ya tanada kafin daga bisani ya gabatar da huduba da harshen larabci.

Bayan haka suma daya bayan daya gwamnonin jihohi da mai martaba sultan na Damagaram sun gudanar da wani takaitaccen jawabin barka da salla ga al’ummar jihar.

Wannan sallah dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da cutar Covid-19 lamarin kuma da ya rage armashin sallar masamman ga magidanta da ke kukan rashin kudi.

Wakilinmu Yakuba Umaru Maigizawa ya rawaito mana cewa za’a ci gaba da bukukuwan karamar sallar har nan da kwanaki uku masu zuwa kamar yadda aka saba a al’adance.

Ku kalli hotunan yadda sallar idi ta kasance:

Continue Reading

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 324,396 other subscribers.

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!