Connect with us

Labarai

Jiragen yaƙi na sojoji sun kashe shanu 1000 a jihar Nassarawa

Published

on

Harin da wasu jiragen yaƙin rundunar sojin saman ƙasar nan suka kai a wani matsugunin fulani makiyaya a yankin ƙananan hukumomin Keana da Doma a jihar Nassarawa, ya yi sanadiyar mutuwar shanu guda dubu ɗaya.

 

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, fulanin da aka kashewa shanun sun bayyana cewa lamarin ya faru ne tsakanin ranakun alhamis goma ga wannan wata na yuni zuwa lahadi goma sha uku ga wata.

 

Labarin da jaridar ta Daily Trust ta ruwaito ya kuma nuna cewa, wasu fulani makiyaya sun jikkata sanadiyar harin.

 

Rahotanni sun ce harin da jiragen yaƙin rundunar sojin saman na Najeriya suka kai ya kwashe tsawon awanni uku yana faruwa, yayin da al’ummar yankin suka tsere sakamakon faruwar wannan al’amari.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!