Connect with us

Labarai

Jiragen yaki na dakarun Operation Hadarin Daji sun kashe ‘yan bindiga

Published

on

Jiragen yaki na dakarun Operation Hadarin Daji na rundunar sojin kasar nan sun kashe ‘yan bindiga da dama a jihar Zamara.

Bayanai sun tabbatar da cewa jiragen yakin sun kuma lalata maboyar ‘yan bindigara dajin Doumborou da ke jihar ta Zamfara.

Rahotanni sun ce maboyar ‘yan bindigar da jiragen yakin suka lalata suna karkashin kulawar wani gawurtaccen dan ta’adda ne da akewa lakabi da Dangote.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun shalkwatar tsaro ta kasa manjo janar John Enenche, ta ce a baya-bayan nan ne dakarun suka samu bayanan sirri game da maboyar ‘yan  bindigar a cikin dajin lamarin da ba tare da bata lokaci ba suka kai musu hari ta sama.

Sanarwar ta kuma ruwaito manjo janar John Enenche na cewa dakarun na operation Hadarin Daji za su ci gaba da shiga lunguna da sakuna na dazukan da ke yankin don kakkabe ‘yan ta’adda.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!