Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shekarau zai fitar da ‘yan kwallo zuwa kasashen waje

Published

on

Tsohon gwamnan Kano kuma sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau yayi alkawarin zai fitar da matasa ‘yan kwallo hazikai biyar, zuwa kungiyoyin kwallon kafa na ketare, daga kungiyarsa ta Shekarau Babes.

Shekarau ya bayyana hakan ne a daren Jumu’a yayin ganawarsa da jagororin kungiyar ta sa a birnin tarayya Abuja.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai mai dauke da sahannun kakakin jagororin kungiyar ta Shekarau Babes Ahmad Babandi Gama.

Sanatan ya tabbatar da cewar kungiyar za ta shiga a dama da ita a gasar rukuni na ‘daya wato Nigeria National League (NNL) na kakar wasa ta 2021/2022.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!