Manyan Labarai
Jirgin Azman ya kasa kwashe fasinjan sa zuwa Lagos
Akalla Fasinjoji 30 ne jirgin Azman ya bari a filin jirgin saman Malam Aminu
Kano sakamakon yadda aka baiwa mutanen da yawansu ya zarce adadin da jirgin zai iya dauka titikin shiga jirgi.
Wasu daga cikin fasinjojin da suka zanta da Freedom Radio sun ce tun a makon da ya gabata ne suka kama kujeru yayin da wasu suka ce sun kama tun makkoni biyu amma aka barsu a kasa.
Sun kuma ce an sanya karfe 7 da rabi na safe a matsayin lokacin da jirgin
zai tashi, kuma da dama daga cikin su sun isa filin jirgin ne tun da misalin
karfe 6 na safe amma aka barsu a kasa duk kuwa da cewa tuni aka shigar da kayan su cikin jirgin.
Daga cikin fasinjojin an samu wadanda suka yi barazanar daukar matakin shari’a kan kamfanin jirgin, inda suka ce barin su a kasa da jirgin yayi ya shafi harkokin su la’akari da cewa suna da muhimmin abin da zasu yi a jihar Lagas, inda can ne jirgin ya nufa.
Wani daga cikin ma’aikatan jirgin na Azman da ya bukaci ya sakaye sunan
shi ya ce matsalar ta faru ne tun jiya da daddare, inda da misalin karfe 9 na
dare jirgi mai diban mutum 124 ya sauka da nufin diban wadannan mutane da safe to amma tun da fari kamata yayi jirgi mai daukar mutane 148 ne zai debe su.
Ya kuma ce tuni aka sauyawa wadancan mutane lokacin da jirgi zai debe su, idan kuma an samu wadanda basa son lokacin da aka sauya musu to za’a yi musu ragin kudaden da suka biya da kaso 25, duk lokacin da suka bukaci amfani da tikitin nasu.