Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kada Allah ya bani lamuni matukar nasan masu aitaka ta’addanci a jihata – Matawalle

Published

on

Gwamanan jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle ya ce, bashi da masaniya kan wadanda ke tayar da zaune tsaye a jihar.

Gwamna Matawalle na bayyana hakan ne lokacin da yake karbar lambar karramawa ta Khadimu Kur’an wadda cibiyar nazarin karatun Alku’ani ta bashi a Lahadin nan.

Muhammad Matawalle, yayin jawabin nasa yayi rantsu da Alkur’ani mai girma kan cewa bashi da masaniyar masu ta’addanci ko kuma masu hannu a aikata ta’addanci a jihar.

“Ina son duk dan Zamfara wanda yake so a kawo karshen matsalar tsaro ya fadi irin abinda na fada, ya ce, ni Bello Matawalle idan ina da hannu ko na sa ni ko ina jin dadin abinda ke faruwa ko nasan wadanda ke kulla abinda ke faruwa kada Allah ya kada Allah ya bani lamuni ko na sakan daya” a cewar sa.

Wannan dai na zuwa ne sakamakon yadda ake samun yawaitar ayyukan ta’addanci a jihar Zamfara.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!