Labarai
Kaduna: Ƴan sanda sun kama mutane 26 da ake zarginsu da yin garkuwa da mutane

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ta kama mutane 26 da ake zarginsu da yin garkuwa da mutane tare da gano bindigogi na gida guda huɗu da kuma kuɗin fansar da mutanen suka karɓa.
Mai magana da yawun rundunar DSP Mansir Hassan, ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a Alhamis ɗin makon nan.
Sanarwar ta ce, jami’an ’yan sanda tare da hadin gwiwar jamiʼan KADVIS ne suka gudanar da samame a yankin Anchau, inda suka kama mutanen su shida wadanda ake zargin su da yin garkuwa da wani mai suna Idris Adamu, mai shekara 60, wanda aka sako shi bayan an karɓi kuɗin fansa na Naira miliyan biyar.
You must be logged in to post a comment Login