Connect with us

Kiwon Lafiya

Kaduna: rundunar yan sanda ta Kama wani da ake zargin yana da hannu a kashe basaraken Adara

Published

on

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna ta kama wani mutum da ake zargi yana da hannu a kashe basaraken kasar Adara Maiwada Galadima a kwanakin baya, a jihar ta Kaduna.

 

A dai watan Oktobar shekarar da ta gabata ne aka kashe basaraken kasar ta Adara Maiwada Galadima akan hanyar sa ta dawowa gida, bayan ya raka gwamna Nasir El-rufai zuwa kasuwar Magani don yin jaje ga wadanda rikicin yankin ya shafa.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan kasar nan DCP Frank Mba.

 

Sanarwar ta ce, mutumin mai suna Abubakar Ibrahim da akewa lakabi da Dan Habu mai shekaru talatin da bakwai, dan asalin yankin karamar hukumar Igabi ne da ke jihar ta Kaduna.

 

A cewar DCP Frank Mba mutumin ya amsa da bakin sa cewa shi mai satar mutane yana garkuwa da su ne, kuma shine ya kashe basaraken kasar ta Adara Maiwada Galadima

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,889 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!