Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan bindiga sun kashe mutane 19 a jihar Kaduna

Published

on

Kimanin mutane 19 ne ake kyautata zaton sun rasa rayukan su a dajin Kukum dake karamar hukumar Kaura a jihar Kaduna, bayan da ‘yan bindiga suka kai musu hari a jiya Lahadi.

Wani ganau da ya nemi a sakaya sunan sa  ya shedawa manema labarai cewa, ‘yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe 10 da rabi na daren jiya Lahadin.

Ka zallika ganau din ya bayyana cewar karin mutum 30 sun sami raunika ya yin da suka yi gudun mun tsira. Shugaban kungiyar cigaban yankin Mr Yashen Titus ya bayyana cewar, an kai harin ne bayan da aka kammala wani fatin bikin aure.

Rubutu masu alaka : 

Sarkin Gusau ya zargi wasu ‘yan Zamfara da taimakawa ‘yan bindiga

Kwana daya da harin Bagwai, ‘Yan bindiga sun kara kai hari a Danbatta

Mr Yashen Titus yana mai cewar, ‘yan bindigar sun je yankin ne dauke da mugan makamai in da suka kashe wadanda ba-su-ji-ba,basu-gani-ba.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna ASP Muhammad Jalige ya tabbatar da afkuwar kai harin yana mai cewa sun sami rahoton ‘yan bindigar sun je yankin ne a daren ranar Lahadi in da suka kashe mutane 19

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!