Connect with us

Labarai

Kafafen yaɗa labarai ne ke kwarzanta matsalolin tsaro –Lai Muhammad

Published

on

Gwamnatin tarayya ta zargi kafafen yaɗa labarai da yin watsi da ƙoƙarin da ta ke yi na yaƙi da ƙalubalen tsaro a ƙasar nan.

Ministan yaɗa labarai da raya al’adu Alhaji Lai Muhammad ne ya bayyana hakan, a wajen bikin sauya sunan kamfanin dillancin Labarai na kasa NAN.

Lai Mohammed, ya ce kafafen yaɗa labarai ne musabbabin da ya janyo ƙarancin masu saka hannun jari daga ƙasashen duniya su ke kaffa -kaffa da ziyartar ƙasar nan.

Ya ce duk wata matsalar tsaro da ake fuskanta a yau galibi yana da nasaba da yadda ‘yan jaridu ke yayata labarin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!