Labarai
Kai-tsaye : Alkali Usman Na’abba ya yi hukuncin rushe kirkirar karin masarautu 4
Babbar kotun jiha mai lamba 8 karkashin jagorancin mai shari’a Usman Na abba ta ayyana cewar dokar da majalisar dokoki tayi na baiwa gwamnatin kano damar kacaccala masarautar kano dokar haramtacciya ce.
Yayin da yake karanta hukuncin mai shari’a Na’abba ya bayyana cewar dukkanin sukar da gwamnati da majalisa suka yi a kunshin shariar ba su da tushe baki daya,
Ya kuma tabbatar da cewar dokar da majalisar tayi ba karbabbiya ba ce a don haka ya rushe dokar.
Tun da fari dai dan majalisar jiha mai wakiltar Gwarzo Hon Nasir Muhammad ne ya shigar da karar yana kalubalantar gwamnatin jiha da majalisar dokokin kano da kwamishinan Sharia akan cewar hanyar da majalisar ta bi a wajen yin dokar ba sahihiya ba ce.
Sai dai masu martani sun yi suka akan hurumin kotun tun a baya kotun ta kuma ayyana cewar tana da hurumin yin Shari’ar.
Jim kadan bayan kammala hukuncin mai shari’a Na abba ya bayyana cewar duk wanda hukuncin bai wa dadi ba zai iya daukaka kara.
Wakiln mu Yusuf Nadabo Isma’il ya zanta da lauyan masu kara Maliki Kuliya wanda yace daman dokar ta san rai ce.
Shi kuwa kwamishinan Sharia Ibrahim Muktar yace za su yi nazari akan hukuncin.
Babbar kotun jaha mai lamba 8 karkashin mai shari’ar Usman Na Abba ta fara karanta hukunci a kunshin shari’ar nan wadda Hon Nasir Muhammad ya shigar yana karar majalisar dokokin jahar ta jiha da gwamnan Kano da kuma babban baturen Sharia na jihar Kano, wato kwamishinan shari’a na jihar Kano Barrister Ibrahim Mukhtar.
Mai karar wanda tsohon dan majalisar dokokin Kano ne yana kalubalantar majalisar dokokin jihar nan bisa yadda yace ta saba ka’ida wajen yin dokar da ta baiwa gwamna damar masarautar kano.
Raba Masarautar Kano: Umarnin kotu baizo mana akan lokaci ba -Sakataren gwamnatin Kano
Siyasantar da masaurata kawai ake son yi-Isyaku Ali Danja
A dai dai wannan lokaci mai shari’a Usman Na abba yana tsaka da karanta hukuncin kuma ana sa ran nan da Awa guda kotun zata kammala karatun daga nan ta bayyana matsayar ta.
ku cigaba da bibiyar shafin don jin yadda shari’ar take gudana