Labarai
Kai-tsaye : Yaushe ne za’a cigaba da sauraran shari’ar Ganduje da Abba
Kotun daukaka kara dake zamanta a Kaduna ta dage cigaba da sauraran karar Jam iyyar PDP da dan takarar gwamnan Abba kabir yusuf wadanda suke kalubalantar nasarar da kotun sauraran kararakin zabe ta ayyana Abdullahi umar Ganduje na Jam iyyar APC a matsayin wanda ya sami nasara.
A dai gobe ko jibi ne alkalin kotun J B Dawood mai darajar SAN zai sanya ranar da zai cigaba da sauraran karar daukaka karar da dan takar jam’iyyar PDP ya shigar gaban ta.
A yayin zaman kotun a dazu nan a Kaduna lauyoyin hukumar zabe J B Dawood SAN sun roki kotun da ta kori daukaka karar sakamakon rashin hujoji masu karfi a yayin shigar da karar.
Wakilin mu na kotu Bashir Muhammad Inuwa ya rawaito cewar lauyan jam iyyar APC Barrister Effiong Effiong ya bayyana cewar basu da suka akan rokon da hukumar zaben tayi.
Amma lauyan Jam iyyar PDP Adebayo Owomolo ya bayyana cewar abun da ya sanya suka daukaka kara shi ne don ganin cewa waccen karar da jam’iyyar PDP ta shigar ba shi da tushe ballanta na makama yayin da ya buga misali da sadara 9 ya kuma karanta wata takardar mai kunshe da sadara 11 da yake nuna cewar suna da hujjoji da ya basu damar daukaka.
An fara gudanar a da shari’ar daukaka karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP Abba Kabir Yusuf ya shigar gaban kotun daukaka kara dake zama a jihar Kaduna.
Sai dai kafin fara saurarn karar lauyoyin bangarorin biyu suna ta musayar yawu kan yadda za’a saurari karar.
Wakilin mu Bashir Muhammad Inuwa da yake cikin kotun ya rawaito cewar lauyan masu gabatar na bangarori biyu ne ke fafatawa.
Kotun daukaka kara dake zamanta a kaduna karkashin alkalai 5 ta sanya yau Litinin18 ga wannan watan na Nuwamba don saurarn karar da Jam iyyar PDP da dan takarar gwamna Abba kabir Yusuf suka shigar ya shigar gabanta.
A halin yanzu kotun daukaka kara dake jihar Kaduna ta shirya don fara sauraran daukak karar da dan takarar gwamnan na jam’iyyyar PDP Abba Kabir Yusuf ya shigar gaban ta yana kalubalantar hukunkunci da mai shari’a Halima Shamaki ta zaratar a watan jiya na Okotoba.
Mai shari’a Halima Shamaki tayi watsi da karar tana mai cewar, karar bata da cikakkun hujoji
Sai dai kawo yanzu an dan sami sabani a tsakanin bangarorin biyu kafin fara sauraran karar.
Wakilin mu na Kotu Bashir Mohammad Inuwa ya rawaito cewar tun daga misalin karfi da rabi na safe harabar kotun ya fara daukar harami.