Labarai
Kai tsaye : Bikin yaye daliban jami’ar tarayya ta Dutse
Mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo na daga cikin manyan bakin da ake sa ran cewar, za su halaci bikin yaye dabai dari 786 na jami’ar tarayya ta Dutsen jihar Jigawa.
Rahotanin sun bayyana cewar, daga cikin daliban da aka yaye dari 786, hamtsin da biyu 52 sun sami digiri mai daraja ta farko wato First Class.
Shugabar jami’ar farffesa Fatima Mukhtar ta bayyana hakan a yayin bikin yaye daliban a yau Juma’a cewa wannan shi ne karo na 5 da jami’ar ta samu nasarar yaye daliban.
Shugaban jami’ar Hajiya Fatima Batulu ta kammala jawabi tana mai cewa, jami’ar ta samu nasarori da dama bayan da aka sami dalibai 55 da suka sa mi daraja ta farko a digirin su na fari.
A halin yanzu mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo na jawabi.
A dai jawabin na mataimakin shugaban kasa ya ce saboda rawar da jami’ar ke takawa ya sanya zata karbi bakwanci babban taron ayyukan gona na bana.
Ku kalli wasu daga cikin hotunan yadda bikin yaye daliban ke wakana a halin yanzu a birnin Dutse.
You must be logged in to post a comment Login