Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Dalilan da suka sanya Buk ta musanta bullar cutar Corona

Published

on

Jami’ar Bayero dake nan Kano, ta musanta labarin da ke cewa an samu bullar cutar Corona a makarantar.

Hakan na cikin wata sanarwa da Jami’ar ta fitar, a jiya wanda ke cewa babu kanshin gaskiya cikin zargin.

Sanarwar mai dauke da sa hannun wani jami’I a ofishin yada labarai na jami’ar ta Bayero Malam Lamara Garba, ta ce, babu wani lamari da ke kama da haka da ya faru a jami’ar.

Tun farko dai jami’ar ta Bayero ta umarci dalibanta a ranar juma’ar da ta gabata da su koma gida sakamakon umarnin da gwamnatin tarayya ta bayar don dakile yaduwar cutar Corona.

Inda kuma jami’ar kai kira ga al’umma da su kaucewa duk wani labara da ka iya fita, idan ba jami’ar ce ta sanar da shi ba

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!