Kaduna
Shugaban Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas ya bayyana sauye-sauyen da shugaba Tinubu ya samar

Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya Tajudeen Abbas, ya bayyana irin sauye-sauyen da Shugaba Bola Tinubu, ya samar domin ci gaban al’umma tun bayan lokacin da aka rantsar da shi a matsayin shugaba.
Tajudeen Abbas, ya bayyana hakan ne a birnin Lagos a lokacin da ya ke gabatar da motoci ga wasu sarakunan gargajiya a yankin kudanci.
Haka kuma, ya ce, sauye-sauyen sun yi tsauri, amma yin hakan ya zama dole domin ci gaban Najeriya.
Tajudeen Abbas ya ce, sauye-sauyen sun samar da daidaituwar farashin canji kudaden waje da bunkasa harkar noma da samar da hanyoyin kudaden shiga ga jihohi.
You must be logged in to post a comment Login