Kiwon Lafiya
Kalaman gwamnan jihar Kaduna kan zabuka ka’ iya sanya a gurfanar da shi gaban kotun hukunta manya laifuka ta duniya
Lauyan nan mai fafutukar kare hakin bil adama Femi Falana mai darajar SAN ya ce kalaman da gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai kan in har masu sanya idanu a zabe suka kuskura suka yi katsalandan a zabukan kasar nan za’a maida gawawakin su zuwa kasashen ka iya sanya a gurfanar da shi a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC.
Lauyan ya ce abunda zai hana a gurfanar da gwamnan na Kaduna a kotun na ICC shi ne ,in an kammala zaben babu ran da aka kashe daga cikin masu sanya idanu na kasashen wajen.
Haka zalika lauyan mai fafutukar kare hakin bil adama ya kalubalanci kasashen Amurka da Burtaniya kan barazana da suke yi ga ‘yan siyasar kasar nan na hana su izinin shiga kasar mussaman ma masu irin kalaman gwamnan Kaduna Nasiru El-rufai
Femi Falana ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da wata mukala a taron da kwamiitin tsaro kan kare hakin bil adama ya shirya don gurmama marigayi Dr, Beko Ransome-Kuti wanda ya mutu shekaru 13 da suka wuce.